Gwamantin Jihar Kano ta na sgirye-shiryen fara kama mabarata manya da yara da ke gararamba a faɗin jahar
BBC Hausa ta ruwaito cewa Shugaban hukumar hana barace-barace ta jihar Sheikh Bakari Mika’il, ne ya bayyana haka inda ya ce dukkan yaran da aka kama hukuncinsu zai rataya ne kan iyayensa.
Haka kuma ya ce akwai tarar kuɗi kamar dai yadda dokar hana bara ta 2013 ta tanada.
To amma kuma wasu daga cikin al’ummar jihar na bayyana ra’ayoyi kan tasirin dokar.