Matar tsohon mataimakin shugaban Najerya Atiku Abubakar, Titi Atiku Abubakar ta ce ba idan Allah ya nufa shekarar 2023 mijinta na iya zama shugaban Ƙasar Najeriya
Jarifar Punch ve ta ruwaito hakan bayan wata zantawa da ta yi da matar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Inda jaridar ta tambaye ta ko zata ta ba mijin na ta shawarar tsayawa takarar shugabancin ƙasar a 2023 ganin cewa ya sha tsayawa amma bai samu nasara ba?
Titi ta bada amsa da cewa, ai komai nufi ne na Allah, ta ƙara da cewa mijin nata ya fara siyasa tun yana makaranta kuma kamar yadda aka sani ɗan siyasa ba ya dainawa gaba ɗaya.
“Babu mamaki wannan karo ya zama shugaban ƙasa shi yasa ya ke ƙoƙarin tsayawa takarar” in ji ta.