Ƴan sanda Sun Kama Mutum Ɗaya Da Ake Zargi Da Kisan Kwamishina A Katsina

Jami’an tsaro a Jihar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya sun tabbatar da kisan gillar da aka yiwa kwamishinan kimiya da fasaha na Jihar Dr Rabe Nasir wanda aka shiga har gidansa dake rukunin gidajen Fatima Shema a birnin Katsina, sannan kuma sun tabbatar da cewa an kama mutum guda da ake zargi ƴana da alaƙa da kisan.

Wannan na zuwa ne bayan ziyarar da kwamishinan Ƴan Sanda Sanusi Buba da Daraktan DSS suka yi a gidan mamacin sakamakon samun labarin faruwar lamarin.

Sai dai ba kamar yanda rahotanni suka ruwaito ba a farko cewa an harbe shi da bindiga, bisa binciken da aka yi an gano cewa an dabawa kwamishinan wuka ne sannan aka janye gawarsa zuwa ban daki aka kulle ta.

Kwamishinan na ƴan sanda ya ce jiya a cikin dare aka kashe kwamishinan amma sai yau sannan aka samu labarin kisan, ya ƙara da cewa an kama mutum ɗaya da ake zargin yana da hannu a cikin kisan.

Ya ce ya zuwa yanzu an ɗauki gawar kwamishinan zuwa Cibiyar kula da lafiya dake Katsina.

An samu bayanan da ke cewa jami’an tsaro sun samu wayar kwamishinan tare da wata da ake kyautata zaton ta wanda ya hallaka shi ce.

Cikin waɗanda suka je gidan kwamishinan harda gwamnan jahar Aminu Masari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram