Sanannen malamin Addinin musulunci, mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi ya furta cewa da ga yanzu zai koma ɗan kallo, ba zai sake cewa uffan ba ko ganawa da ya ke yi da ƴan fashin daji ba domin a samu zaman lafiya ya dawo tsakanin maharan da kuma kawo ƙarshen hare-haren da su ke yi.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Sheikh Gumi ya kasance mai son a yi sulhu tsakanin gwamnati da ƴan bindiga, sai dai kuma a wata hira ta musamman da jaridar ta yi da shi a Kaduna ya bayyana cewa daga yanzu ya tsame bakinsa cikin harkar tun da gwamnati ta aiyanasu a matsayin ‘yan ta’adda.
Babban malamin ya ce Allah ya sani yayi iya kokarinsa na ganin an samu zaman lafiya a yankunan dake fama da matsalar tsaro amma abin ya faskara saboda biyan buƙatar wasu.
Gumi dai kamar yadda aka sha gani a kafafen sada zumunta ya sha kai ziyara cikin daji yana baiwa ƴan bindiga shawarwari a zauna lafiya da juna, ayi sulhu, ya haka kuma ya shawarci gwannatin Najeriya kan yadda za’a shawo kan lamarin ta hanyar ruwan sanyi tare da yafiya ga pan bindigar da gami da samar wa Fulani makiyaya abubuwan more rayuwa.
Sheikh ɗin ya ce tuni ya yanke shawarar daina shiga cikin sha’anin tunda gwamnatin Najeriya ta aiyana ƴan fashin dajin a matsayin pan ta’adda.
Malamin ya ce a baya ya yi kasada da rayuwarsa ya shiga wuri mai haɗarin gaske domin a samu sulhu amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.
Yana mai cewa wasu ƴan bindigar da ya tunkara ƙyas su ke jira su yi harbi amma Allah ya tsare shi ya shiga ya fito lafiya.
Gumi ya ƙara da cewa nan gaba idan aka samu sauyin siyasa zai ci gaba daga inda ya tsaya don a samu kawo ƙarshen matsalolin tsaro a ƙasar ta Najeriya.