Firayiministan Burkina Faso Ya Sauka Daga Muƙaminsa Saboda Matsalar Tsaro

Rahotannin sun nuna cewa Firaiministan Burkina Faso Christophe Joseph Marie Dabire da gwamnatinsa sun yi murabus a sakamakon matsin lamba na al’ ummar ƙasar game da matsalolin tsaro.

Firaiministan da gwamnatinsa sun yi murabus ne a yammancin ranar Laraba a yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar ƙin jini kan da abin da jama’a suka kira, gazawar gwamnati wajen yaƙar mayaƙan jihadi da suka janyo asarar rayuka tare da hana zaman lafiya a asar da ke yankin Sahel.

DW Ta ruwaito cewa wannan shi ne karon farko a nahiyar Afirka da shugaban gwamnati da mambobin majalisa suka yi marabus saboda matsin lamba daga al’ummar ƙasar.

Dokokin ƙasar Burkina Faso, sun tanadi ɗaukacin gwamnatin kasar da ta yi murabus a yanayi irin wannan da aka sami firaministan da ya zabi ajiye mukaminsa, inda gwamnatin za ta kasance ta wucin gadi, har sai an kafa wata sabuwa, kamar yadda babban sakataren gwamnatin ƙasar Stephane Wenceslas Sanou ya jaddada

Shugaban ƙasar Roch Marc Christian Kabore ya shiga hali na tsaka mai wuya a baya-bayan nan, inda ya ke ci gaba da shan suka a sakamakon yawaitar hare-haren mayaƙan da ake zargi ƴan al-Qaeda ne, musanman harin farkon watan Nuwamban da ya gabata, wanda yayi sanadiyar rayukan jami’an sojin ƙasar akalla 49 da ma wasu fararen hula.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram