Kotun da ke shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ta umarci jami’an tsaron gidan gyaran hali da su bar shi ya sanya hannu domin fitar da ƙuɗi daga asusun ajiyarsa na banki.
Wannan na zuwa ne bayan zaman ci gaba da sauraron shari’ar da malamin ya ke fuskanta.
Kotun ta ce a ba shi damar fitar da ƙuɗin don ya ciyar da iyalinsa.
Freedomradio ta ruwaito cewa, a yayin zaman kotun an gabatar da shaida na 3 wato sufeto Muhd Kabiru daga hedikwatar ƴan sandan jahar Kano wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi bincike akan tuhumar da ake yi ma malam Abduljabbar ɗin.
Saidai Abduljabbar Kabara ya soki shaidar bayan ya yi masa tambayoyi ya kuma roƙi kotu da ta yi watsi da abinda shaidar ya faɗa.