Wasu ƴan bindiga sun je har gida sun hallaka kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha na jahar Katsina Dr. Rabe Nasir.
Lamarin dai ya faru a cikin daren jiya inda suka dira gidansa da ke cikin rukunin gidajrn Fatima Shema a cikin birnin Katsina suka kashe shi.
Bayanan da mu ke samu yanzu haka ana ƙoƙarin ɓalle ƙofar ɗakinsa don a fito da gawarshi.