Shugaba Buhari Ya yi Tir Da Allah-wadai Da Kisan Gilla Da Aka Yi Ma Kwamishina A Katsina

Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana game da kisan da aka yi a jiharsa ta Katsina a ranar Alhamis inda aka kashe kwamishinan kimiyya da fasaha Dr. Rabe Nasir.

Garba Shehu wanda shi ne ke magana da yawun shugaban ƙasar ne ya fitar da sanarwar hakan, sanarwar ta ce Shugaba Buhari ya ce kisan kwamishinan mummunan abu ne kuma abin tir ne inda ya ƙara da cewa irin waɗannan mugan ayyukan ba su da mazauni a ƙasar.

Buhari ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su gudanar da bincike tare da tabbatar da cewa an yi hukunci kan waɗanda aka kama da laifin kisan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram