Wasu ƴan bindiga da suka kai farmaki a GRA na Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna da sanyin safiyar ranar Asabar sun Sha da kyar, a lokacin da sojoji suka amsa kiran kawo agajin gaggawa.
Tun da farko ƴan bindigar ɗauke da makamai sun ƙona wani gida, bayan sun gaza yin awon gaba da mai gidan.
Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa ƴan bindigar sun mamaye al’ummar garin ne da misalin ƙarfe 12:30 na safiyar Asabar, amma sojoji suka shiga tsakani jim kaɗan bayan hakan.
Rahotanni sun bayyana cewa, ƴan bindigan ne suka fara buɗewa jami’an sojojin wuta, inda daga bisani suka miƙa wuya ga irin ƙarfin wuta na rundunar soji.
Wani mazaunin garin mai suna Bilyaminu ya ce ƴan bindigar sun ƙona wani gida kuma suna shirin kai farmaki gida-gida ne a lokacin da sojoji suka iso yankin.
“Mun gode wa Allah da Sojoji suka zo a kan lokaci, idan ba haka ba da labarin ya yi muni domin su ƴan bindiga sun zo ɗaukar mai gidan ne, amma aka yi sa’a gidan babu kowa, sai dai sun banka wa gidan wuta saboda takaici,” inji shi.
Jaridar Daily Trust Ta ruwaito cewa ƴan bindigar sun kai wa al’ummar garin hari kwanaki biyu da suka wuce, inda suka tafi da wani mutum da matarsa da kuma ɗiyarsa.
An kuma ruwaito cewa rikicin harbe-harben bindiga da ya ɗauki tsawon awa ɗaya ana yi tsakanin sojoji da ƴan ta’addar ya haifar da tashin hankali a cikin al’ummar garin na Sabon Tasha.
sai dai duk yunƙurin da aka yi wajan samun Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ASP Jalige Mohammed ba’asami domin jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.