Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Imo sun ce masu garkuwa da mutane sun sako basaraken gargajiya na tsohuwar masarautar Mbutu da ke Mbaise, mai martaba Eze Damian Nwaigwe.
An yi garkuwa da Nwaigwe ne da sanyin safiyar Alhamis daga fadarsa da ke Mbutu.
Ƴan bindigar wadanda yawansu ya haura 10, sun afkawa Mbutu ne a ranar Alhamis din da ta gabata inda suka yi awon gaba da basaraken a fadarsa, kamar yadda wata majiya ta al’ummar da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce an sako sarkin ba tare da jin rauni ba, kuma tuni ya koma ga iyalansa.
Sanarwar dai ba ta bayyana inda aka sako sarkin ba, ko an kama wadanda suka yi garkuwa da shi, ko kuma an biya kudin fansa.
Sanarwar ta ce, “Bayan mai martaba, HRH Eze Damian Nwaigwe na Masarautar Mbutu, wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 09/12/2021 da misalin karfe 03:00 na Rana a gidansa, an kubutar da shi ba tare da jin rauni ba kuma ya sake haɗuwa da iyalansa.
Nwaigwe ya yi sa’a yayin da aka kashe takwaransa na Masarautar Njaba, Edwin Azike, wanda aka yi garkuwa da shi ranar Juma’a.
An jibge gawar Sarkin a dandalin kasuwa da ke cikin Garin da lamarin ya faru..