Ƴan ISWAP Sun Yi Garkuwa Da Matafiya Da Dama A Hanyar Damaturu Zuwa Maiduguri

Mayaƙan ƙungiyar IS dake Kai farmaki a yammacin Afirka (ISWAP) sun yi garkuwa da wasu fasinjoji da ba a tantance adadinsu ba a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da safiyar Assabar.

A cewar wata majiyar tsaro, fasinjojin sun nufi Maiduguri da ke jihar Borno daga Damaturu a Yobe, inda aka tare su a wani wuri dake kusa da garin Benishiek.

“Eh, an kai hari a kan masu ababen hawa a safiyar yau a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, wadannan marasa hankali sun yi awon gaba da wata da fasinjojin da ba tantance adadinsu ba a kewayen Benishiek da Mainok.

Ba mu da ƙarin cikakkun bayanai fiye da wannan. ” Majiyar ta ce.

Shugaban kungiyar fararen hula ta Arewa maso Gabas, Amb Ahmed Shehu, ya shaida wa manema labarai cewa shi ma ya samu rahoton sace fasinjojin.

“Yanzu na sake samun labarin yin garkuwa da mutane a hanyar Damaturu-Maiduguri a safiyar yau. Me ya sa ba za mu iya samun mafita mai ɗorewa ga wannan bala’in da ke faruwa ba?” Amb Shehu ya tambaya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar ranar Asabar.

A baya-bayan nan ne ƴan ta’adda suka yi awon gaba da fasinjoji a jihar da ke daɗa zama tamkar wata cibiyar ƴyan ta’adda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram