Atiku Ya Ce Buhari Bai San Dabarun Samar Da Shirin Ci Gaba A Ƙasa Ba

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya Atiku Abubakar ya ce salon da dabarun ci gaba, da Shugaba Buhari ke aiwatarwa don co gabn ƙasar ba akan dai-dai yake yin su ba.

Atiku ya ce tsarin ci gaban ba ya haifar da ɗa mai ido maimai haka ma yanzu ya haifar da ƴara miliyan 13 da basa zuwa makaranta da kuma dimbin matasa marasa aikin yi son haka ya kama a sake duba tsarin.

Tsohon shugaban ƙasar yana maganar ne a yayi da ya ke bayani a wurin wata Lakca da aka shirya mai taken “Ilmi da iko” a Jami’ar Achievers dake Owo, Jahar Ondo, inda bayyana cewa shirin ci gaba wanda ba shi ya kamata a riƙa amfani dashi ba a ƙasar shi ya ƙara taimaka wa wajen wanzuwar rashin tsaro a ƙasar.

Atiku ya ce ƙasar na buƙatar ta riƙa amfani da tsare-tsaren ci gaba ta hanyar la’akari da yawan al’ummarta don amfanin kowa da kowa.

Ya ce mallake komai da Gwamnatin tarayya ta yi shi ne haifar da matsaloli barkatai a ƙasar.

Ya na mai cewa cin hanci da son yin kuɗi dandanan ga matasa ba tare da sunyi wani aiki ba ya samu ne dalilin rashin ƙirƙire-ƙirƙire da kuma gasa a tsakanin Jahohi ta hanyar zuwa da ayyukan yi da kuma samar da sana’o’i maimakon haka sai suka zura ma Abuja ido domin samun kuɗaɗe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram