Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewar dole a tilastawa iyaye su tura ƴaƴen su zuwa Makaranta.
Atiku a lokacin da yake gabatar da wata Lakca a taron yaye ɗaliban Jami’ar Achievers dake Owo a Jahar Ondo, yace ƙasashen da suka zuba maƙudan kuɗaɗe a ɓangaren ilmi da fasahohi sune ke kan gaba a Duniya.
Yace idan aka sanya ilmi ya zamanto kowa zai iya samun sa a Najeriya, to ƙasar zata cigaba, kuma zata magance wasu matsaloli dake fuskantar ta.
“Ilmi shike wayar da kawunan mu tare da buɗe mana ido domin fahimtar Mahallin mu da duniyar mu, yana taimakawa wajen haɓɓaka tattalin arzikin mu, tare da fahimtar matsalolin dake fuskantar Al’ummar mu, da ƙasar mu da duniya, da kuma yadda zamu magance su” inji shi.
“Ilmi abune dake da matuƙar amfani, ƙasashen da suke martaba ilmi tare da zuba maƙudan kuɗaɗe a wajen shi, suna magance al’amuransu.
“Abu da yafi hakan, shine ilmantar da mata yafi mahimmanci. Bincike ya nuna cewa domin al’umma ta cigaba, dole ta ilmantar da mata sabudda abubuwan da ke tattare da hakan.
Yace idan iyaye suna tura ƴaƴan su makaranta, adadin yaran da basa zuwa makaranta zai ragu.