Fashewar Tukunyar Iskar Gas Ta Jikkata Manya Da Ƙananan Yara A Abuja

Akalla mutane biyar ne da suka haɗa da ƙananan yara uku suka samu munanan raunuka sakamakon fashewar wani bututun iskar gas da kuma wuta da ya kama a ƙaramar hukumar Gwagwalada da ke babban birnin tarayya Abuja.

Fashewar ta faru ne a unguwar Dagiri da ke kusa da hanyar Lokoja zuwa Abuja a Gwagwalada.

Shaidun gani da ido sun ce an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Zamad da ke unguwar

Shedun gani da idon sun Kuma shaida wa Majiyar Jaridar Jakadiya cewa an samu matsala ne a lokacin da wani abokin ciniki ya zo sayan iskar Gas ɗin, inda kuma yake ta waya a kusa da wurin.

“Ba za mu iya cewa da gaske ga abin da ya faru ba, amma duk da mukaji shine fashewace ta auku”. In ji su.

An Kuma ruwaito cewa, Aƙalla shaguna hudu ne gobarar ta shafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram