Gwamnan Ebonyi Ya Dakatar Da Babban Sakatare A Jahar.

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bayar da umarnin dakatar da babban sakataren ma’aikatar ƙananan hukumomin jihar, da al’amuran masarautu da raya karkara saboda jinkirin biyan albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a watan Nuwamba.

Umahi ya kuma bukaci kwamishinan ƙananan hukumomin da harkokin masarautu da raya karkara na jahar da SSA da SA a kan ƙananan hukumomi da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ta hanyar tabbatar da cewa an biya ma’aikata albashin da ya kamata daga yanzu.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Dakta Kenneth Igwe a ranar Juma’a, wanda aka rabawa manema labarai kwafin sanarwar a ranar Asabar.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa “A bisa haka ne gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da babban sakatare na ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu da raya karkara da kuma Akanta JAAC na tsawon wata daya ba tare da biyan sh albashi ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa rashin bin umarnin gwamnan zai janyo wata matsalar babba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram