Rundunar ƴan sanda a jahar katsina ta ce ta kama matasa 16 da ta ke zargi da sata a yayin da ake kan aikin gina gadojin ƙasa da za a yi a ƙofar ƙaura da ƙofar ƙwaya wanda gwamnatin jahar ta gaddamar a kwanakin baya.
Mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan a yayin da ya ke gabatar da su ga menama labarai a hedikwatar ƴan sandan da ke Katsina.
Gambo Isha ya ce sun kama matasan su goma sha shida a ƙofar ƙaura inda ake gudanar da aikin yayin da su kuma matasan su ke ta faman tone wayoyin fitilun bakin titi da sauran abubuwan da suka tari gabansu.
“Sun yi ɓarna ba ƙaramar ɓarna ba, wasu daga ciki sun gudu da waɗannan kayayyaki amma Allah ya ba mu nasar daga ciki mun kama guda 16 kamar yadda ku ke gani.
Kalli Matasan a cikin bidiyo
To saidai a lokacin da ake tambayar matasan duk babu wanda ya amsa laifin da ake zarginshi da shi, kowane ya ce hanya ce ta kawo shi sai aka yi rashin sa’a jami’an ƴan sandan suka kama shi.
Kafin kama matasan dai kafafen sada zumunta sun rinƙa ankarar da mahukunta cewa matasa fa na yi ma al’umma sata a wurin da ake gudanar da aikin.