Tsohon gwamnan jahar Sokoto a Najeriya Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nuna rashi jin daɗinsa kan kashe-kashen al’umma da ƴan bindiga ke yi a yankin, yana mai kira ga Shugaba Buhari da “ya ji tsoron haɗuwarsa da Allah”.
BBC ta ce, Tsohoin gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata hira da ta yi da shi kwanaki kaɗan bayan ƴan fashin daji sun ƙona wata motar bas ɗauke da mutum kusan mutum 30 a cikinta a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Sokoto.
Bafarawa ya ce: “Wajibi ne Buhari ya bi al’umma a zauna a tattauna kamar yadda ya bi su gida-gida lokacin da yake neman ƙuri’a, saboda mu taimaka masa wajen haɗuwarsa da Allah.”