Shugaba Muhammadu Buhari na Najeria ya jaddada ƙudirin Gwamanatisa na magance ƴan bindiga daɗi, gami da kare ƴan ƙasa daga duk wani nau’in ta’addanci.
Buhari ya bada tabbacin a ranar Juma’a a lokacin da tawagar da ya tura ta kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Aminu Tambuwal akan kisan matafiya 23 da ƴan ta’adda suka yi, ta hanyar ƙona su.
Wannan tabbaci na zuwa ne a cikin wata sanarwa da Mai baiwa Gwamnan Sokoto Shawara na Musamman akan kafafen yaɗa labarai Malam Muhammad Bello a ranar Asabar a Sokoto.
Saƙon shugaban ya fito ne daga shugaban tawagar Gwamnatin Tarayya kuma Mai bada Shawara akan tsaron Ƙasa Manjo-Janar Babagana Monguno mai ritaya.
Monguno ya yabawa Gwamna Tambuwal daya fasa tafiyar da yayi niya domin ya karɓi tawagar sgugaban ƙasar duk da an sanar dashi a ƙurarren lokaci.
“Mun zo ne Sokoto akan wani al’amari wanda shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarce mu, domin mu jajanta maka, da Al’ummar Sokoto, gami da Sultan na Sokoto Alhaji Sa’ad Abubakar III , akan mummunan lamarin daya faru a makonni da suka gabata.
“Shugaban Ƙasa yaji wannan lamari cikin rashin jindaɗi, inda aka rasa rayuka ba tare da laifin komai ba. Duk rayuwar wani ɗan ƙasa tana da amfani, shiyasa haka ya sanya Shugaba Buhari cikin halin rashin jindaɗi na wannan mummunan al’amari.
“Shugaban Ƙasa na miƙa saƙon ta’aziyya ga akan rasa rayuka da akayi, yana kuma tausaya wa akan haka, tare da bada tabbacin cewa an kama waɗanda suka yi wannan mummunan aiki, da kuma zartar masu da hukunci.
Shugaban Ƙasa ya umarci duk wata hukuma ta tsaro dake da alhaki, dasu tashi tsaye domin gano masu aikata wannan lamari, bawai na wanda suka yi wannan kisa ba, har da duk abubuwan da suka faru a Jahar.
“Duk wani Babban Hafsan Tsaron na Ƙasar muna tare dashi a wannan tafiya, wanda hakan na nuna cewa Shugaban Ƙasa na son magance wannan matsala ta tsaro, domin al’ummar Sokoto su samu natsuwar gudanar da rayuwar su,” aka naƙalto Monguno na cewa a cikin sanarwar.
Dayake maida jawabi, Gwamnan Jahar Sokoto yace Jahar na cikin wani mummunan yanayi na fama da ayyukan ƴan bindiga daɗi, da masu garkuwa da mutane, wanda suke ta tsoratar da mutane.
Tambuwal yace al’amarin yaƙi da Rundunar soji ta “Operation Hadarin Daji” keyi a Jahar Zamfara, ya kawo ƴan ta’adda sun bar dazuzzukan su, zuwa Sokoto.
Yace lamarin yafi muni a Ƙananan Hukumomin Sabon Birni da Tangaza, da Illela da sauran wasu Ƙananan Hukumomi a Jahar.