Wasu Kaji 2 Matan Wani Zakara Sun Kwantar Da Hankalin Mijinsu Ta Hanyar Haɗa Kan Ƴaƴansu.

Daga Umar Usman

Akasin yadda al’ada ta gudana, dangantaka ta halittu ba ta wuce ace wane ɗan wane uwa ɗaya uba ɗaya, ko kuma uba ɗaya, ko uwa daya uba kowa da nasa, su kuwa waɗannan kajin uwarsu 2 ubansu ɗaya.

Wannan lamari yafaru a wata unguwa da ke a nan cikin birnin katsina da ake kira bayan yan katako, a gidan gonar Dr. Mukhtar el-kasim.

Wasu kaji na Hausa da zakaran su guda ɗaya, suka fara nasa kwai tare, kuma a waje ɗaya,a gurbi ɗaya.

Wani abin ƙarin al’ajabi shine, tare sukayi kwanci, wannan ta yi zuwa wani lokaci gudar ta amshe ta, a haka har suka ƙyanƙyashe ƙwayayensu guda 10 da suka yi babu dakwaye ko ɗaya.

Haka suka cigaba da rainon ƴaƴan, amma ba wanda zai iya tantance ko rabewa tsakanin ƴaƴan, kowace daga cikin iyayen ya’yan na bin ta a baya.

Da mu ke zantawa da mai kajin, Mukhtar el-kasim, yace ” ban yi tunanin za’a samu ƴaƴa a cikin ƙwayayen ba, tunda na ga sun yi wannan shirme, amma cikin ikon Allah ka ga sun kammala kwancinsu babu Wanda ya lalace”. In ji shi.

Saurari Fira Da Mai Kiwon Kajin:

Ya ƙara da cewa, akwai darasi sosai a cikin wannan lamari, musamman a kan iko da tasarrufi na Allah, wanda ya ke yin yadda yaso a cikin halittunsa.

A taƙaice sudai ƴantsakin basu iya gane wacece uwarsu sai dai 4 daga cikin su sun mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram