Ƴan bindiga sun Kashe wani limamin coci reverend Dauda Bature bayan da suka karbi kudin fansa daga hannun mai matarsa.
RFI ta ce, rahotanni sun nuna cewa,ƴan bindigar sun yin awon gaba da Dauda Bature da mai ɗakin ne ranar 8 ga watan Nuwamba a lokacin da yake cikin gonar sa dake yankin Rigasa a karamar hukumar Igabi.