Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya jajanta ma gwamnati da mutanen ƙasar Amurka kan iftila’in guguwa da ta kashe sama da mutane 100 a jihohi shida.
BBC ta ce, A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce ya damu ƙwarai kan yadda gidaje da makarantu da wuraren sana’o’i da asibitoci suka lalace.
Shugaban ya yi kira ga mutanen Najeriya su taya sauran mutanen duniya addu’a ga waɗanda suka rasa ransu da kuma samun sauƙin wadanda suka jikkata.
Sama da mutane 100 ne suka mutu a guguwar wadda ta fi ɓarna a jihar Kentucky ta ƙasar ta Amurka.