Buhari Ya Lashi Takobin Ɓiƙa Mulki Ga Duk Wanda Ya Lashe Zaɓen 2023

Shugaba Buhari na Najeriya ya bayyana aniyarsa ta miƙa mulki ga duk wanda Allah ya ba sa’ar lashe zaɓen shugaban ƙasa a kakar zaɓen shekarar 2023.

Buhari ya tabbatar da haka ne ga ƴan Nijeriya cewa lallai zai yi duk mai yiwuwa don ganin an yi sahihin zaɓe zai kuma tabbatar da ya miƙa ya hannanta mulki ga duk wanda ya lashe zaɓen.

Martaba FM ta ruwaito cewa, mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina ne ya faɗi haka a wurin wani taron ƙarawa juna sani kan Dimokraɗiyya wanda shugaban Amurka Joe Biden ya shirya ta yanar gizo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram