Gwamna Tambuwal Na Zargin Sojojin Najeriya Kan Hare-haren Sokoto

Gwamnan Aminu Waziri Tmbuwal na Jihar Sokoto dake Najeriya ya zargi sojojin ƙasar da baiwa ƴan bindigar da aka fatattaka a Jihar Zamfarar damar share wurin zama a Sokoto inda suke kaiwa mutanen jahar hare hare ba jingirtawa, abinda ke basu damar hallaka jama’a kullu yaumin.

Wannan na zuwa bayan munanan hare haren da ƴan bindigar suka kai a ƴan kwanakinnan ciki harda wanda suka kona mutane 42 a cikin mota a karamar hukumar Sabon Birni.

RFI ta ce, Tambuwal wanda ke jawabi lokacin da ya karbi tawagar jaje da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa jihar, ya bayyana cewar Jihar Sokoto na cikin mawuyacin hali dangane da ayyukan waɗannan ƴan ta’addan dake kashe mutane a koda yaushe.

Gwamnan wanda ya nuna damuwarsa akan yadda sojojin Najeriyar suka ƙaddamar da aikin Tarwatsa ƴan ta’addan Jihar Zamfara ba tare da tintiɓar jihohin dake makotaka da ita ba, yace aikin da suka yi a Zamfara ya sa ƴyan ta’addan sun fantsama zuwa jihar Sokoto inda suke cin karensu babu babbaka.

Tambuwal yace ya dace ace an gudanar da aikin karkade mayakan lokaci guda a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Neja domin hana su samun mafaka a wasu yankunan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram