Da ga ranar 14 ga watan Disamba na shekarar 2021 Gamwantin Najeriya ta ce za ta dakatar da jirage da ga ƙasashen Canada, Britaniya da Saudiyya shigowa Ƙasar.
Hadi Sirika wanda shi ne Ministan Harkokin Sufurin Jirgin Sama ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin nan a Legas.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ce, Sirika ya yi ya faɗi cewa gwamnati ta sanya takunkumin ne a matsayin ramuwar gayya bisa ga dakatar da jirage da ga Nijeriya da ƙasashen su ka yi sakamakon ɓullar sabon nau’in korona na Omicron.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ƙasar nan za ta sanya waɗan nan ƙasashe ukun a matsayin waɗan da za a sanyawa idanu sakamakon ɓullar Omicron ɗin.