An bada rahoton yadda ƴaƴan wani ɗan shekara 56 a su uku a Kenya, suka kashe mahaifin na su da duka, bisa zargin ɓalle gidansu, tare da satar wayar hannu, da suka saya a tare.
Bayan sun kashe mahaifin na su da duka, sun jefar da gawar sa kusa da daji.
Wasu ƴan mata guda biyu ne suka ga gawar yayin da ke kan hanyarsu ta zuwa Makaranta.
Joyce Nankezho, ƴar uwar marigayin tace ” Marigayin yana zama a Nairobi, yazo ne binne gawar wani maƙwabcin sa, wanda ya rasu a ƴan kwanakin baya. Yana ɗaya daga cikin wanda suke haƙa kabarin maƙwabcin daya rasu a lokacin da ɗan sa ya kira.”
Kakar yaran Leonida Keya ta bayyana cewa sun zo ne gidan ta domin su ci abinci a ranar da suka aikata lamarin, amma basu faɗa mata abinda suka yiwa mahaifin na su ba.
Keya tace “Wannan lamari ya girgiza Ni, na zauna tare da waɗannan yaran, tun lokacin da suka rabu da mahaifin nasu, amma ban taɓa tunanin zasu iya kashe shi ba”. In ji ta.
Kakamega OCPD David Kabeya Wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewar an kama yaran, kuma ana tsare dasu a ofishin ƴan sanda na Kakamega.