Ƙungiyar Izala ta Najeriya ta bayar da umarni ga mambobinta cewa su fara gabatar da al-qunut saboda matsalar tsaro da ake fama da shi a Ƙasar.
Shugaban Ƙungiyar na ƙasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bada umarnin a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta.
Sheikh Bala Lau ya na mai cewa umarnin ya shafi dukan masallatan da ke Najeriya mallakar ƙungiyar da kuma duk wasu wurare na karantarwar ƙungiyar.
Hakazalika ya ce hatta mata da ke zaune a gida suma su bi umarni tare da yawaita azkar da nufin Allah ya tausaya game da halin da ake ciki.
Malam Bala Lau ya ce an ɗauki wannan mataki da kyakykyawar niya tare da tsammanin Allah zai amsa ya yi maganin ƴan ta’adda da ma su ɗaukar nauyinsu.
Sanarwar ta kuma ce umarnim zai fara aiki ne nan take ba tare da wani jinkiri ba.