Ƴan bindiga Sun Yi Yunƙurin Garkuwa Da Mutane A Hanyar Abuja

Ƴan bindiga sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna da yammacin jiya Lahadi.

Wani da ya shaida lamarin, Mai suna Ibrahim Umar, ya shaida wa jaridar SAHELIAN TIMES cewa, suna tafiya ne a cikin motoci sai ‘yan bindigar suka fara harbe-harbe a kansu.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:25 na daren jiya. akan babbar hanyar Abuja, kusa da kauyen Rijana.

Umar ya shaida cewa ‘yan bindigar sun kashe mutane da ba a tantance adadinsu ba da ke tafiya a cikin mota kirar Peugeot J5.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram