Ministan harkokin ƴan sandan Najeriya Maigari Dingyadi ya ce ba zai yiwu Shugaba Buhari ya je jaje ko ina ba saboda ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga a kasar.
Ministan ya yi wannan batu ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa game da sha’anin tsaro wanda ta ɗora muryar firar a shafinta na Facebook.
A cikin firar an tambayi Dingyadi cewa mutanen Arewa na nuna rashin jin daɗinsu ganin yadda Buharin bai je Sokoto da Katsina ya yi jaje ba da kanshi sai ma aka gan shi ya shilla jahar Legas inda ya halarci taron ƙaddamar da wani litta da kuma jajantawa game da wani yaro ɗan makaranta da ake zargin an kashe.
Dingyadi ya amsa da cewa, “No ai kasan waɗannan abubuwan kullum suna cikin faruwa kuma bai yiwuwa ace shi Shugaban Ƙasa ya iya zuwa ko ina waɗannan abubuwan suka faru to shi yasa maimakon ka fara abinda kake ganin bai yiwuwa ai idan ka tura wakili kamar kai ne ka je.
Kuma kafin ma ya tura ya yi saƙo na musamman na jaje ya kuma ba ƴan Najeriya tabbacin cewa za a ɗauki matakai na musamman don ganin an shawo kan waɗannan mataalolin” In ji shi.
Ministan kuma ya ambata cewa ko shakka babu abubuwan da ke faruwa suna damun gwamnati amma dai ba su biwaye ta ba kuma tana kansu Insha Allahu.