Bayan Shafe Shekaru 13 Tsohuwar Matar Adam Zango Ta Dawo Harkar Fim

Bayan shafe kimanin shekara 13 da ta bar masana’antar Kannywood, jaruma Amina Uba Hassan, tsohuwar mata ga jarumi Adam A. Zango ta dawowa harkar fim.

Tsohuwar jarumar ta fara fitowa a fina-finai tun farko-farkon shekarar 2000, daga bisani ta auri Adam A. Zango a shekara ta 2007.

Wata biyar bayan ta haifi ɗa namiji a shekarar 2008 tare da Adam Zangon sai auren nata da shi ya mutu.

Bayan sun rabu jarumar ba ta ci gaba da harkar fim ba, sai a kwana nan ta fito a eani shiri mai dogon zango wanda kamfani 2Effects ya shirya, mai suna ‘Gidan Danja’.

“Yana da matuƙar wahala ga uwa kuma bazawara a ce bayan shafe shekaru masu yawa ka dawo yadda kake a masana’antar fim, na dauki tsawon lokaci ina shawara kafin na sake dawowa. Fitowa a fina-finai shi ne abin da na fi so, shi ya sa na dawo,” in ji ta.

Madogara: Jaridar Aminiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram