A rahoton da muka samu Shugaba Muhammadu Buhari yana kan ganawa da Gwamna Aminu Tambuwal na jahar Sokoto dangane da sha’anin tsaro a jahar.
Mai taimaka ma shugaban ƙasar kan kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmed ne ya sanar da haka a shafinsa na Facebook.
Bashir Ahmed ya ce shugaba Buhari na ganawa da Tambuwal ɗin ne da daddaren nan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Sokoto dai ta shiga cikin jerin jahohin Arewa da ke fuskantar matsalar aikace-aikacen ƴan bindiga da ke faruwa a yankin Arewacin ƙasar.
Ko a satin da ya gabata ƴan ta’adda sun tare mota ɗauke da matafiya inda suka ƙona matafiyan kimanin mutum 42 da ma wasu hare-haren da suka kai daga baya.