EFCC Ta Bankaɗo Wani Sirri Na Wani Gwamna A Arewa Da Ya Ɗebi Tsabar kuɗi Naira Biliyan 60

Hukumar da ke yaƙi da masu yi ma tattalin arziƙin ƙasa ta Najeriya, EFCC, ta ce ta bankaɗo wani gwamnan wata jaha a Arewacin kasar da ya rarumi tsabar kuɗi har naira biliyan 60 daga asusun jiharsa.

BBCHausa ta ce, hukumar ta bayyana haka ne a saƙon da ta saba aika ma manema labarai a kowane wata, mai taken EFCC Alert.

EFCC, wadda ta ambato shugabanta Abdulrasheed Bawa yana yin ƙarin bayani game da batun a hirarsa da mujallar da hukumar take wallafawa, ta ce gwamnan da aka gano na wata jiha ce da ke Arewa ta Tsakiya ko da yake bai faɗi sunansa ba.

Zan iya gaya muku a kyauta cewa sabon sashen da muka bude kan leƙen asiri yana aiki tukuru.

cikinsu shi ne wani gwamna a wata jiha ta Arewa Ta Tsakiya, inda suka gano cewa cikin shekara shida da suka gabata (mutum ɗaya) ya cire tsabar kuɗin da suka kai N60 bn.”

“Muna kallon abubuwan da yake yi, kuma ina tabbatar muku cewa bayan mun kammala bincike, za mu sanar da ‘yan Najeriya kan abubuwan da muka yi a bayan fage game da laifukan da ake aikatawa ta amfani da shafukan intanet…,” in ji Bawa.

Jahohin Arewa ta tsakiya dai sun hala da Filato da Binuwai da Kogi da kuma Kwara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram