Gwamnati Najeriya Ta Ce Za Ta Kara Kuɗaɗen Haraji A Shekarar 2022

Ministar Kuɗi ta Najeria Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa da yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta ƙara kuɗaɗen harajin da take karɓa daga shekara mai zuwa ta 2022.

Shamsuna Ahmed da ta bayyana hakan ta ce akwai yiwuwar ƙara kason da ake karɓa na kuɗaɗen haraji daga ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni a a shekarar mai zuwa saboda halin matsin da tattalin arziƙin Najeriya ke ciki.

Tsarin dokar kuɗi ya yi tanadin sauyi a hajarin kuɗaden shigar mutane, harajin yin sayayya (VAT), harajin kan sarki, dokar harajin ribar kamfanoni, dokar kuɗaɗen shikgar kamfanoni, dokar kafa hukumar FIRS da sauransu,” Ta ce.

Jaridar Aminiya ta ce, Ministan ta sanar da haka ne a ranar Litinin ɗin nan a jawabinta ga masu ruwa da tsaki a lokacin taron sauraron ra’ayoyin jama’a kan Ƙudurin Dokar Kuɗi da Majalisar Wakilai ta shirya a Abuja.

Ministar ta kuma bayyana cewa akwai sauye-sauye da dama da ƙudurin dokar kuɗi ya tanada, waɗanda za su fara aiki a tsakiyar shekara mai zuwa.

Ta ce sauye-sauyen sun shafi ɓangaren kudɗaɗe sannan ma’aikatarta ta karɓi shawarwari a kansu daga wurin masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram