Mutane 15 Sun Tsere Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Jahar Sokoto

Kusan mutane 15 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Sokoto sun tsere daga hannun wadan da suka yi garkuwa da su.

Daya daga cikinsu, jami’in fasaha ne da ke aiki da wani kamfani mai kula da harkokin sadarwa a ƙaramar hukumar Isa ta jihar wanda aka yi garkuwa da shi makonni biyu da suka gabata.

Wani na kusa da shi ya ce lamarin ya ritsa da shi a yayin da wasu ƴan bindiga dauke da makamai suka ɗauke shi da karfi a tsakanin karamar hukumar Isa da Sabon Birni a kan hanyarsa ta duba wata matsala ta sadarwa da ta faru.

Da yake ba da labarin yadda wanda aka kama ya tsere, ya ce ya yaudare ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka bari ya tsare shi cewa yana so ya samu sauƙi yayin da sauran ƴan bindigar suka tafi wani wurin.

Hakazalika Shugaban ƙaramar hukumar Isa, Abubakar Yusuf ya tabbatar wa manema labarai da kuɓutar wasu mutane 14 da aka yi garkuwa inda ya shaida cewa a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a wani asibitin garin.

Mazauna yankin sun ce waɗanda harin ya rutsa da su sun tsere ne daga wani sansanin ƴan bindiga masu biyayya ga babban ɗan bindigar nan Bello Turji da ke da alhakin kai hare-hare a yankin ‘yan majalisar dattawa na gabas da ke Sokoto da kuma wasu sassan jihar Zamfara.

Shugaban ya ce mutane 11 daga cikin waɗanda suka tsere ƴan Sokoto ne yayin da sauran ƴan jahar Zamfara ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram