Tashin Gobara Ya Lalata Dukiya Ta Milyoyin Naira A Ikeja

Rahotanni sun bayyana cewa tashin wata gobara ya lalata dukiyoyi na miliyoyin naira a yanki mai lamba 18, Titin Otigba, a ƙauyen Computer dake Ikeja.

Gobarar data fara tashi da sanyin safiyar Litinin din nan, ta mamaye wani rukunin kantuna inda ta lalata kayayyaki masu daraja.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, har yanzu ba a san musabbabin barkewar tashin gobarar ba.

Jami’an hukumar kashe gobara sun zo cikin gaggawa wanda hakan ya hana gobarar cinye wasu gine-gine dake wurin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, CSP Adekunle Ajisebutu, yace an tura ‘yan sanda zuwa wurin domin kare ‘yan kwana-kwana da sauran su al’ummar yankin.”

Kazalika “An samu nasarar kashe gobarar. sai dai ba a samu asarar rai ba a lamarin, amma duk da haka gobarar ta lalata dukiyoyi masu mahimmanci waɗanda ba a san kiyasin ba tukuna.

Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin gobarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram