Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki kasuwar Pinau da ke yankin Pinau a karamar hukumar Wase a jihar Filato, inda suka kashe mutane 11 tare da jikkata wasu da dama.
An ruwaito cewa ƴan bindigar sun kai hari kasuwar ne da yammacin ranar Lahadi.
Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa, a ranar 8 ga watan Disamba, ta ruwaito yadda mazauna wasu kauyuka suka koka da kwararar ƴan bindiga a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Wase.
Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa akwai masu ba da labari a cikin al’ummomin da ke aiki tare da ƴan bindigar.
Shapi’i Sambo, shugaban matasa a Wase, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust harin na baya-bayan nan, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa a cikin kwanaki 10 da suka gabata ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama a yankin tare da karɓar miliyoyin naira a matsayin kuɗin fansa.
Ya ce, “Suna karɓar kudin fansa a miliyoyi. Wani lokaci suna karɓar Naira miliyan biyu, wani lokaci kuma Naira miliyan biyar. Kwanaki ukun da suka gabata sun karɓi Naira miliyan 5 kafin su sako wani mutum da suka yi garkuwa da shi kwanakin baya.”
“Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, bai amsa kira da SMS ba a lokacin da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakinsa kan lamarin” inji Daily Ttust.