An Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Kogi

Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta tabbatar da yin garkuwa da Mrs Seriya Raji, mahaifiyar shugaban ma’aikatan gidan gwamnan jihar Yahaya Bello.

Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da Misis Raji a yammacin ranar Litinin a gidanta da ke Nagazi, dake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Adavi a jihar Kogi.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, kwamishinan ƴan sandan jihar Kogi, CP Idrisu Dauda Dabban, ya ce mutanensa sun yi wa yankin da kuma garuruwan kan iyakokin jihar da Edo ƙawanya da nufin ceto mahaifiyar shugaban ma’aikatan.

Dabban ya ba da tabbacin cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an kama wadanda suka yi garkuwa da matar, tare da kuɓutar da ita.

Kwamishinan ƴan sandan ya buƙaci dukkan jami’an ƴan sanda da su sa ƙaimi wajen gudanar da bincike da kuma ceto matar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram