Birtaniya Ta Cire Najeriya Daga Jerin Ƙasashen Da Ta Sanya Ma Ta Kunkumin Hana Shiga Ƙasarta Dalilin Omicron

Hukumomin Burtaniya sun kammala yanke shawarar sake duba dokar hana zirga-zirgar da aka sanya wa Najeriya da wasu ƙasashe 10 a daidai lokacin da aka gano cutar Corona Nau’in Omicron.

Sajid Javid, Sakataren Lafiya na Burtaniya ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa majalisar dokokin Burtaniya bayani a yau Talata.

Ya shaida wa ‘yan majalisar cewa Ingila za ta cire dukkan ƙasashe 11 daga cikin jerin ƙasashen masu hadarin yada cutar daga ƙarfe 4:00 agogon GMT a ranar Laraba.
Sakataren Lafiya ya ce dokar hana wasu ƙasashe shiga ƙasar Bai da Wani amfani wajen dakatar da yaduwar sabon cutar Corona Samfarin Omicron.

Ya ce: “Don haka zan iya ba da sanarwar yau cewa yayin da za mu ci gaba da ɗaukar matakan gwaji na wucin gadi don balaguron ƙasa da kasa, za mu cire dukkan kasashe 11 daga jerin kasashen da muka haramta shiga ƙasarmu daga ƙarfe 4 na safen gobe.”

idan za’a iya tunawa asu daga cikin ƙasashen da Birtaniya ta Haramtawa shiga ƙasar irin su: Angola, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Namibia, Najeriya, Afirka ta Kudu, Zambia da Zimbabwe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram