Masu Zanga-Zanga A Katsina Sun Buƙaci Masarautar Daura Da Ta Dakatar Da Naɗin Sarautar Da Ta Ke Shirin Yi Ma Ɗan Shugaba Buhari

Masu zanga-zanga a Katsina sun buƙaci hukumomi da su hanzarta kama manyan ƴan ta’adda 2 da suka addabi Arewa tare da kira ga Masarautar daura da ta gaggauta dakatar da naɗin sarautar da ta ke shirin yi ma Yusuf ɗan shugaba Buhari.

Zanga-zangar wadda wasu matasa suka gudanar a Katsina a ranar Larabar cikin lumana sun yi ta domin nuna fushinsu game da abubuwan da ke faruwa na ta’addanci a Arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

Duk da dai Zanga-zangar ta samu tsaiko inda kwamishinan ƴan sandan jahar ya dakatar da matasan bisa zargin cewa ba su bi hanyar da ta dace ba wajen gudanar da zanga-zangar, Bashir Dauda wanda shine ya jagoranci lamarin ya shaida ma manema labarai cewa, mamufar zanga-zangar ita domin jahwo hankalin gwamnatin tarayya da ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kawo ƙarshen matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

Dauda ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su jajirce su tabbatar da sun kama manyan ƴan ta’adda biyu da suka fi haɗari wato Dogo Giɗe da Bello Turji domin gurfanar da su gaban shari’a, ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun san maɓoyarsu.

Daga ƙarshe ya yi kira ga masarautar Daura da ta gaggauta janye ƙudurinta na yin bikin naɗin sarauta da zata yi ma ɗan shugaba Muhammadu Buhari wato Yusuf Buhari a kwannan nan inda ya ce saboda yanayin da al’umma suke ciki na rashin tsaro.

Wata majiya da Jakadiya ta tuntuɓa a masarautar da Daura ta shaida cewa har inda yau ta ke ba ta san da labarin naɗin sarautar da ake cewa ba ” yanda kaga katin gayyatar a saman soshiyal midiya nima haka na gamshi” in ji majiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram