Tsaro: Babu Zancen Jam’iyya APC Ko PDP Kowa Ya Damu – In ji Kwankwaso

Tsohon gwamnan jahar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce aikace-aikacen ƴan ta adda na ƙarabta’azzara abyankin Arewa.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata fira da BBC ta yi da shi wanda ta ɗora bidiyon a shafinta na Facebook a ranar Talatar nan.

Tsohon gwamnan ya ce “an san inda suke zaune amma abin mamaki yau zai ka ji su can gobe ka ji su can sai ka ji su can sau da yawa ma sai su ɗauki mutane su tafi da su kuma duk dajin nan ma fa ba wata nisan duniya ne ba Chaina ko wani wuri ba a babur su ke ɗauka su tafi da mutane” ya faɗa.

Kwankwaso ya ce ƴan ta’adda sun yi suna wasu ma sun fi manyan jami’an tsaro suna, wanda ya ce lokacin da suka fara kuwa makaman su ma zuwa su ƙwata a wurin jami’an tsaron amma yanzu sun giga.

Ya ce sau da yawa sai ka ji an ce sun zo akan babur ɗaruruwa, to sojojin Najeriya nawa ne sannan ƴan sandan Najeriya nawa ne? “Kwanan nan fa kowa ya ji cewar an kai ƴan sanda sama da dubu 30 jahar Anambara a je a yi zaɓe, ai waɗannan inda yanda ake da kyakykyawan tsari ne da daga can Anambaran sai a wuce da su Ko Sokoto ko Zamfara ko Kebbi Ko wani wuri wanda ake da irin wannan matsaloli”. Ya bayyana.

Sanata Kwankwaso ya ƙara da cewa wannan lamari na matsalar tsaro babu zancen APC ko PDP ko wata jam’iya ya shafi kowa da kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram