Wani Hatsarin Mota Ya yi Sanadiyar Rasa Rayukan Mutane 20 A Bauchi

Mutane 20 ne suka mutu a hatsarin motoci guda biyu a jihar Bauchi.

A hatsarin na farko, mutane 16 sun kone kurmus bayan da wata motar bas Toyota Hummer ta yi karo da wata tirela a kauyen Bambal da ke kan titin Kano zuwa Jama’are ranar Lahadi.

Bayan mintuna 30, mutane hudu sun mutu sannan wasu bakwai suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya faru a kauyen Duhuwar Kura dake kan hanyar Azare zuwa Zaki.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatarwa manema labarai cewa hadarin na farko ya faru ne da misalin karfe 7:00 na dare.

Motar mai dauke da kujerun Fasinjoji 18 ta yi karo da wata tirela kuma ta tashi da wuta, inda ta kona fasinjoji 16 da ba a iya gane su ba.

Abdullahi ya ce mutane 11 ne suka shiga cikin lamarin na biyu kuma an garzaya da wadanda suka mutun zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Azare, inda wani likita ya tabbatar da mutuwar mutane hudu.

Ya kuma gargadi masu ababen hawa da su guji gudun wuce gona da iri domin gujewa hadarurruka a hanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram