Akwai Ƙura: Bashin Da Ya Maƙare Wuyan Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan 38

Jumullar kuɗin da ake bin Najeriya a bashi ya kai naira tiriliyan 38, kwatankwacin dala biliyan 92.75 kenan zuwa rubu’i na uku na bana wato watan Satumba, wanda adadin ya ƙaru da kashi 18 cikin 100 kan kuɗin da ake bin ƙasar a bara.

BBC Hausa ta ce, Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya ruwaito ofishin kula da basussuka na Naeriyar wanda ya bayyana hakan a ranar Talata.

Najeriya dai na na ci gaba da karɓar bashi domin gudanar da manyan ayyuka da kuma farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar wanda ke ƙoƙarin farfaɗowa daga matsin da ya shiga sakamakon karewar farashin ɗanyan man fetur a kasuwar duniya da kuma tasirin annobar korona.

Jumullar bashin da ake bin ƙasar zuwa rubu’i na uku na 2020 ya tsaya ne a naira biliyan 32.22.

Sai dai ƙasar ta sayar da takardun lamuni a watan Satumba domin aiwatar da kasafin kuɗinta da kuma ƙara darajar kuɗaɗenta a asusun ƙasashen waje wanda hakan ya sa aka samu ƙaruwa da kashi 7 cikin 100 na bashin da ake bin ta a rubu’i na biyu na bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram