ASUP Tayi Barazanar Sake Shiga Yajin Aikin Da Ta Dakatar

Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na Ƙasar nan – ASUP tayi barazanar dawo wa yajin aikin data dakatar, sakamakon zargin ƙin cika alƙawari da Gwamnatin Tarayya tayi, bisa ga yarjejeniyar da suka sanyawa hannu tsakanin su da Gwamnatin a watan Afrilun Shekarar 2021, domin kawo ƙarshen yajin aikin su.

Malaman sun buƙaci Gwamnati ta sakar masu Naira biliyan 15 da aka amince za’a sakar masu domin gyaran Makarantu, gami da kuɗaɗen Ariyas na watanni 10 da Malaman Makarantu a Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na Ƙasa suke bin Gwamnatin Tarayya.

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a ƙarasa cika yarjejeniyar da aka cimmawa a Shekarar 2010.

ASUP tayi wannan roƙon ne a cikin wata takardar bayan taro da aka cimma matsaya a taro karo na 16 da aka gudanar a Asaba Jahar Delta, tsakanin 6 zuwa 10 ga watan Disamba, kuma aka sanar dashi ga Manema Labaru a ranar Laraba a Abuja.

Taron shugabannin ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar ASUP Comrade Anderson Ezeibe, domin duba nasarar da ƙungiyar ta cimmawa a taron ta
da masu riƙe da Kwalejojin Kimiyya da Fasaha na Gwamnati a faɗin Ƙasar.

ASUP ta shaidawa ƴan Najeriya dasu ɗora alhakin hakan ga Gwamnatin Tarayya, idan har Malaman suka dawo yajin aikin da suka dakatar.

ASUP ta kuma yaba da ƙirƙirar sabbin cibiyoyi guda 6 a Kwalejojin Kimiyya da Fasaha guda 6 wanda Asusun Tallafawa Ilmi TETFund ya gina.

Akan hare-hare da ake kaiwa a Makarantu, tare da sace Ɗalibai da Malaman su, Ƙungiyar ta nuna damuwarta akan yawaitar matsalolin tsaro dake fuskantar ƙasar, wanda ke kawo tsaiko ga zaman lafiya doka, da lumana, gami da jindaɗin ƴan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram