An ci gaba da yin zanga-zanga bisa ga nuna kin jinin rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Martaba FM ta ruwaito, yau ma a jahar Kano wasu mutane sun fito domin yin zanga-zangar kuma da yawansu matasa ne.

A ƴan kwanakin nan dai kusan jahohin da ke Arewa kalan ne ba a samu waɗanda suka fito zanga-zanga ba saboda matsar tsaro da ke addabar yanki.
Ko a jiya ma an so a yi zanga-zangar a Katsina sai dai jami’an tsaro sun shawo kan lamarin kafin ya yi ƙamari.
A kano dai wata matashiya mai suna Zainab ta shirya zanga-zangar lumana a kwanan nan sai dai daga bisani ta nisanta kanta daga zanga-zangar bayan da DSS suka gayyace ta ofishinsu.