Mutumin Da Ke Auren Mata 59 Da Ƴaƴa 300 A Enugu Ya Mutu

Mutumin nan ɗan asalin jahar Enugu da yayi ƙaurin suna wajen auren mata da yawa mai suna Simon Odo mai laƙabi da ɗan shaiɗan wanda ya auri mata 59 tare da haihuwar ƴaƴa 300 da jikoki ma su tarin yawa ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.

Ɗaya daga cikin fitattun ƴaƴasa mai suna Emeka Odo ne ya tabbatar da mutuwar baban nasa ga menema labarai a ranar Talatar nan, ya ce har ma an fara shirye-shiryen rufe mamaci.

Emeka ya ce mahaifin nasa ya kasance ba shi da lafiya tsawon makonni uku kenan, ” Yanzu haka muna kan tattaunawa da dangina don ganin yadda za mu yi shirye-shiryen rufe shi duba da umurnin da ya bari na cewa kar mu kai shi wuraren ajiyar gawa” in ji ɗan nasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an ce yanzu haka al’ummar yanki sun taruwa a bakin babban gidansa domin yi ma iyalin da ya bari gaisuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram