Yanzu-Yanzu: Ƴan ta’adda Sun Kashe Rilwanu Gadagau Ɗan Majalisar Dokin Jahar Kaduna, Sun Yi Awon Gaba Da Matafiya

Ƴan ta’adda sun kashe ɗan majalisar dokokin jahar Kaduna Rilwanu Gadagau, a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Gadagau, shine ke wakiltar ƙaramar hukumar Giwa ta jahar Kaduna.

A samu labarin cewa ƴan ta’addan sun kashe shi ne a ranar Litinin da daddare a yayin da suka tare matafiya a kan hanyar, sai dai ba a ga gawarshi ba sai da safiyar ranar Larabar nan.

Har yanzu ƴan sanda ba su ce komai ba game da mutuwar ta shi amma wani makusancin mamacin ya shaida ma gidan talabijin na Channels faruwar hakan.

Ya ce an ga gawar ɗan majalisar dokokin ne a kusa da wani ƙauye da ake kira Mawai wanda bai fi nisan kilo mita 13 ba tsakaninsa da cikin birnin Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram