An Rufe Gawar Mutumin Da Ke Da Mata 59 A Cikin Mota Tare Da Kunna Mashi Waƙar Da Ya Fi So Don Taya Shi Fira

An yi jana’izar wani mawaki a Najeriya mai suna Simon Odo, wanda kuma aka fi sani da “King of Satan” ta hanyar bizne shi a cikin karamar motarsa a kauyensa da ke jihar Enugu bayan mutuwarsa yana da shekaru 74.

An bar motar a kunne sannan aka saka wakar da Odo ya fi so a cikin motar wadda ta kasance a matsayin akwatin gawarsa.

Jama’a sun ce wannan shine karo na farko da suka taba ganin irin wannan jana’iza a kauyen na Aji.

Dan mamacin, Uchenna Odo ya ce, Mr Odo ne ya bukaci a rufe gawarsa ta wannan hanya a lokacin da yake raye.

Wasu kadan daga cikin danginsa da sashen harshen Igbo na BBC ya yi hira da su a kauyen Aji, sun bayyana marigayi Odo a matsayin mutumin kirki wanda ya yi kokarin kauce wa duk wani abin da zai bata tsakaninsa da sauran mutane.

Mr Odo dai ya mutu ne da safiyar ranar Talata bayan gajeruwar rashin lafiya.

A wata hirarsa da BBC a shekarar a 2020, Odo ya ce yana da mata 57 da ‘ya’ya da jikokin da ba zai iya tuna yawansu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram