EFCC Ta Sake Bankaɗo Wani Sabon Asusun Diezani Maƙare Da Sama Da Dala Miliyan 72 A Najeriya

Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC ta bankaɗo wani sabon asusun ajiyar tsohuwar ministar man fetur ta ƙasar Diezani Allison Madueke da ke ɗauke sama da da la miliyan 72 a Bankin Fidelity.

Hukumar EFCC ce ta bayyana haka bayan da ta kama tsohon shugaban bankin Nnamdi Okonkwo wanda ya jagorance shi lokacin da Madueke ke rike da muƙamin minista a kasar.

Tsohuwar ministar dai ta kasance a jerin sahu na gaba gaba a tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ta shugaba Goodluck Jonathan kuma ta gudu daga Najeriya domin kaucewa tuhume-tuhume da dama da ake mata akan zargin cin hanci da rashawa, yayin da Hukumar EFCC ta kwace wasu daga cikin kadarorin da ta mallaka.

RFI ta ruwaito cewa, mai magana da yawun Hukumar Wilson Uwujaren ya sanar da gano kuɗaɗen a asusun ajiyar Diezani da kuma damƙe tsohon manajan bankin.

Uwujaren ya ƙara da cewa an kuma yiwa Okonkwo wanda yanzu ke jagorancin Bankin First Holding tambayoyi dangane da wasu kuɗaɗen da suka kai Dala miliyan 153 da wasu Dala miliyan 115 na daban.

Kakakin hukumar yace tuni suka ƙwato Dala miliyan 153 daga ajiyar ta, yayin da ake ci gaba da tafka shari’a akan dala miliyan 115 wanda ake zargin an ware su ne domin baiwa jami’an Hukumar zabe cin hanci.

Uwujaren yace yanzu haka Okonkwo tare da wani Charles Onyedibe na komar EFCC saboda sabon asusun ajiyar dake kunshe da sama Dala miliyan 72 da aka gano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram