Wasu rahotannin sun bayyana cewa an dakatar da ‘yan kasar Koriya ta Arewa daga yin dariya da shan barasa na tsawon kwanaki 11 domin bikin cika shekaru goma da rasuwar tsohon shugabansu Kim Jong II.
Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa, wannan umarni daya haramta wa ‘yan Koriya ta Arewa nuna farin ciki, hukumomin gwamnati ne suka bayar da shi domin tunawa da mutuwar Kim Jong II, wanda ya mulki kasar daga shekarar 1994 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2011.
Bayan mutuwarsa, shugaban na yanzu Kim Jong Un, ɗansa na uku kuma ƙarami, ya karɓi ragamar shugabancin kasar.
“A lokacin zaman makoki, bai kamata mu sha barasa ba, ko mu yi dariya ko kuma shagaltuwa da sha’awa,” kamar yadda wani dan Koriya ta Arewa daga birnin Sinuiju dake kan iyaka da arewa maso gabashin Asiya ya shaida wa gidan rediyon Free Asia.
Majiyar ta kara da cewa, “A baya, an kama mutane da dama suna shan giya ko kuma suna buguwa a lokacin zaman makoki, ana daukarsu a matsayin masu aikata miyagun akida wanda hakan yasa aka tafi dasu bayan haka ba a sake ganin su ba.
“Ko da danginku ya mutu a lokacin zaman makoki, ba za a barku ku yi kuka da babbar murya ba, kuma dole ne a fitar da gawar bayan an gama.
“Mutane ba za su iya yin bikin ranar haihuwarsu ba idan sun fada cikin lokacin zaman makoki.”
Majiyar ta kuma bayyana cewa an haramtawa ‘yan Koriya ta Arewa zuwa siyayyar kayan abinci a ranar 17 ga watan Disamba – daidai da ranar da tsohon shugaban ya mutu.