Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Femi Gbajabiamila ya taya Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar sa, inda ya cika shekaru 79 a duniya.
Ya taya Buhari murna akan ɗumbin ayyukan da ya yiwa Najeriya tun lokacin da ya hau mulki daga shekarar 2015, yana mai bayyana cewa irin wannan mutumen dole ƴan Najeriya zasu taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
Gbajabiamila ya yabawa Shugaba Buhari akan sanya Najeriya a gabansa, kafin wani abu, yana mai cewa ƴan Najeriya na Alfahari dashi.
Yace a cika shekaru 79, Shugaba Buhari ya cimma abubuwa a rayuwa, da kuma a matsayin sa na shugaba, daya ke da nagarta.
Gbajabiamila yayi amanna cewa Shugaban Ƙasa zai yi abubuwa masu tarin yawa ga Ƙasar, a ƴan kwanakin da suka rage a Gwamnatin sa.
Ya bayyana tare da farin cikin yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya cika alƙawurran da ya ɗaukar wa Jam’iyyar APC.
“Shugaban Ƙasa, Najeriya da ƴaƴan ta na Alfahari dakai, musamman ta yadda kake jagorantar Ƙasar, abun a yaba ne.
“A saboda haka, nake bin sawun miliyoyin ƴan Najeriya wajen tayaka murnar cika shekaru 79, tare da fatan ƙarin lafiya,” inji shugaban Majalisar Wakilai