Hukumar Kwastan A Kano Da Jigawa Ta Kama Fatar Jaki 339 Da Harajinta Ya haura miliyan 31 Da Ba A Biya Ba

Hukumar Kwastam ta Najeriya, shiyar Kano da Jigawa, ta bayyana cewa ta tara kuɗaɗen shiga da ya kai N25.3billion a shekarar 2021, fiye daga N24.4billion da rundunar ta samu a shekarar 2020.

Rundunar ta ce ayyukan da take yi a filin tashi da saukar jiragen sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA) ya kuma ƙara haɓaka kuɗaɗen shiga.

Kwanturolan hukumar, Suleiman Pai Umar ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, rundunar ta kuma samu nasarar daƙile ayyukan fasa-kwaurin da ta kai ga kama wasu haramtattun kayayyaki da suka kai sama da Naira Milliyan 187 a matsayin darajar harajin su a ayyukan ta na baya-bayan nan.

Kazalika ya ce, Daga Cikin kayayyakin da hukumar ta ƙwace akwai, buhunan shinkafa 1040 na kasar waje da kuɗin su ya Kai naira miliyan 69 da katon-katon na spaghetti na ƙasashen waje da darajarsu ta kai Naira miliyan 63.9, da kuma fatar jaki 339 da ta haura Naira miliyan 31.

Sannan ya ce a dai cikin shekarar ta 2021, rundunar ta kama jimillar mutane 398 tare da haramtattun Kayayyaki na sama da Naira biliyan 1.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram